Majalisar Dinkin Duniya Ta Ce Duniya Ta Shirya Tunkarar Wata Sabuwar Annoba

2020-12-29 11:10:45
Majalisar Dinkin Duniya Ta Ce Duniya Ta Shirya Tunkarar Wata Sabuwar Annoba

A cikin wani bayani da babban sakatare janar din MDD Antonio Guterres ya yi a yayin bukin ranar Annoba ta duniya ta farko ya fadi cewa:

“Ya kamata duniya ta dauki darasi game da Annobar cutar Covid -19 mai saurin kisa, kana ya bukaci a yi gagarumin shiri domin tunkarar sabuwar Annobar da za ta bulla anan gaba.”

Har ila yau ya kara da cewa wannan bukin farko na ranar Annoba ta duniya ya fado ne a karshen shekara, kuma acikin wani yanayi da mutane da yawa suke jin tsoro sosai na zuwan wannan bala’I sai ga shi ya zama gaskiya.

Daga karshe ya nuna cewa adaidai lokacin da muke murmurewa da kokarin ganin bayan Anoobar da ake ciki ya zama dole mu yi tunani game da abin da zai zo a nan gaba.Kana ya jinjina wa likitoci da ma’aikatan lafiya da ke sahun gaba game da namijin kokarin da suke yi wajen tunkarar Annobar Korona Virus a fadin duniya.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!