Kasar Faransa Ta Tabbatar Da Kashe Sojojinta Guda 3 A Kasar Mali

2020-12-29 10:58:10
  Kasar Faransa Ta Tabbatar Da Kashe Sojojinta Guda 3 A Kasar Mali

Fadar Iliza ta kasar Faransa ta fitar da wata sanarwa da ke tabbatar da kashe sojojinta guda 3 a kasar Mali a ranar litinin da ta gabata , bayan da motar da sojojin suke ciki ta yi karo da wani abin fashewa da aka dasa akan hanya a yankin Hamburi da ke tsakiyar kasar ta Mali.

Ofishin shugaban kasar ta faransa Emanuel Macron a cikin wani bayani da ya fitar ya jinjinawa sojojin da suka rasa ransu a filin daga , kana ya jaddada matsayin kasar game da kokarin da take yi na yaki da ta’adanci , sai dai wannan yana zuwa ne adai dai lokacin da babu wata kungiya da ta sanar da alhakin dana bomb din da yayi sanadiyar mutuwar sojojinta.

Kimanin sojojin faransa guda 47 ke nan aka kashe a kasar Mali ,a shekara ta 2013 ne kasar Farasan da ta aike dasojojin ta guda 5000 zuwa kasashen Mali Chadi Niger Borkina - Faso da fakewa da dalilan fada da ta’addanci.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!