Kungiyar Kwallon Kafa Ta Chelsea Da Aston Villa Sun Yi Canjaras 1-1 A Wasan Premier Da Suka Buga
2020-12-29 10:55:12

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta kasa hawa mataki na gaba a gasar Premier bayan da ta yi kunnen doki daya da daya da abokiyar karawarta Aston villa a wasan da suka buga a jiya da dare.
Chelasea ta zura kwallon farko ne da misalin minti 34 da fara
wasa ta hannun dan wasanta Olivier Giroud bayan da Ben chiwell ya bugo masa
inda ya sa kai ya dokata a ragar Aston villa.
Sai dai ita ma
kungiyar kwallon kafa ta Aston vila ta farke cin ne bayan minti biyar da zura
mata kwallon, inda dan wasanta Anwa El Ghazi ya kwace kwallo daga hannun mai
tsaron gidan chelasea bayan da aka auno ta .
Yanzu dai sakamakon ya
nuna cewa chelsea da Aston villa za su ci gaba da kasancewa a matsayi na 5 da 6 a teburi, kafin wasan da
aka shirya za’a yi a yau talata tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Manchester
city da kuma Everton, sai dai an dage wasan zuwa wani lokaci saboda kara
tsanantar cutar korona Virus a kasar.
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!