Afirka Ta Kudu: Adadin Masu Kamuwa Da Corona Yana Karuwa

2020-12-28 20:40:17
Afirka Ta Kudu: Adadin Masu Kamuwa Da Corona Yana Karuwa

Gidan Rediyon Faransa ya bayar da rahoton cewa, Sabbin alkaluman da ma’aikatar lafiyar kasar Afirka ta kudu ta fitar sun nuna cewa a halin yanzu yawan masu cutar ta coronavirus a Afrika ta Kudu ya kai miliyan 1 da dubu 4 da 413, daga cikinsu kuma cutar ta kashe dubu 26 da 735.

A makon jiya kididdigar hukumomin lafiya ta nuna cewar, akalla mutane dubu 11 da 700 ake ganowa sun kamu da cutar kowace rana tsawon kwanaki 7 jere da juna.

Sake barkewar annobar ta coronavirus karo na 2 a Afrika ta Kudun ya sanya hukumomin kasar soma shawara kan yiwuwar sake yi wa jama’a kulle bayan dakatar da zirga-zirga, matakin da ake sa ran shugaban kasar Cyril Ramaphosa zai sanar yayin jawabin da zai yiwa ‘yan kasar a tsakiyar makon da muke shiga.

Kawo yanzu akalla mutane dubu 62 da 649 annobar coronavirus ta aika barzahu, daga cikin miliyan 2 da dubu 658 da 646 da suka kamu da cutar.

Morocco ce kasa ta 2 da annobar tafi yiwa ta’adi bayan halaka mata mutane dubu 7da 240, daga cikin dubu 432da 79 da suka kamu.


015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!