Putin Da Jinping: Alaka Tsakanin Rasha Da China A Yanzu Tafi Karfi Fiye Da Kowane Lokaci A Tarihi

Shugabannin kasashen Rasha da China
sun bayyana cewa, alaka tsakanin kasashensua
halin yanzu, tafi karfi fiye da kowane lokaci a tarihinsu.
Tashar RT ta bayar da rahoton cewa,
a wata zantawa da suka yi yau ta wayar tarh, shugaban kasar Rasha Valdimir
Putin, da kuma takwaransa na China Xi Jinping, sun yaba da gagarumin ci gaban
da aka samu a alakarsu a dukkanin
bangarori.
Shugabannin kasashen na Rasha da
China sun ce ko shakka babu, yanayin da ake ciki a halin yanzu a fagen siyasar
duniya, da kuma kalubalen da kasashen biyu suke fuskanta daga kasashen da suke
neman mayar da duniya mallakinsu, hakan yasa dole ne su dunkule domin tunkarar
wanann kalubale.
Putin ya ce Rasha da China suna yin
aiki tare a bangarori na siyasa, tattalin arziki kasuwanci da musayar ilimi
tsaro da sauran bangarori na ci gaban al’ummominsu, amma ba a taba samun wani
lokaci da kasashen biyu alakarsu ta yi karfi kamar wanann lokacin ba.
A nasa bangaren shugaban kasar China
ya sheda wa Putin cewa, China da Rasha za su ci gaba da gudanar da komai nasu a
tare domin samar da daidaito a cikin harkoki
nasiyasa duniya.
015