​Najeriya: Manyan Kasashen Duniya Ne Masu Amfana Da Matsalar Tsaro

2020-12-28 19:32:33
​Najeriya: Manyan Kasashen Duniya Ne Masu Amfana Da Matsalar Tsaro

Wasu daga cikin masana kan harkokin tsaro da siyasar kasa da kasa, sun yi imanin cewa manyan kasashen duniya ne suke amfana da matsalar tsaro a Najeriya.

Tun bayan da shugaba Buhari na Najeriya ya karbi ragamar shugabancin kasar a cikin shekara ta 2015, ya sanar dad aura damara ta yaki da ‘yan ta’adda na Boko Haram, inda bayan wasu lokuta ma ya sanar da cewa ya yi nasarar murkushe su.

Abubuwa da suka yi ta faruwa bayan wanann sanarwa da shugaba Buhari ya bayar, sun tabbatar da cewa wadannan ‘yan bindiga suna nan, kuma suna ci gaba da aikinsu na ta’addanci

Bisa yadda sauran kungiyoyin ‘yan ta’adda masu da’awar jihadi suke gudanar da lamurransu na ta’addanci da kisan gilla a kan ‘yan adam musulmi da wadanda ba musulmi ba, hakan ya tabbatar da cewa kungiyar Boko Haram ba ta da wani banbanci da irin wadannan kungiyoyi.

Abin da jama’a da dama suke yin tambaya a kansa wanda kuma har yanzu an kasa samun amsa a kansa shi ne, su wane ne suke tafiyar da lamarin wannan kungiya da kuma daukar nauyinta, da sama mata makamai da kuma horar da mayakanta?

Dangane da sauran kungiyotin ‘yan ta’adda takwarorin kungiyar Boko Haram masu samar das u da daukar nauyinsu da makudan kudade da makamai da horar da su, da kuma masu ba su fatawa a bayyane suke, su ne manyan kasashen turai da manyan kasashen larabawa.

Kungiyar Boko Haram wadda ta fadada ayyukanta daga Najeriya zuwa sauran kasashen da suke makwabtaka da ita, tana samun kayan aiki da kudade ta hanyoyin da ba a bayyane suke ba, to amma kuma abin da yake saka shakku kan lamarin shi ne, me yasa har yanzu an kasa murkushe kungiyar, duk kuwa da cewa gwamnati tana kashe makudan kudade kan haka, kuma manyan kasashen turai da Najeriya take dasawa da su, suna da’awar cewa suna bayar da taimakon da ya kamata a wannan fage, amma babu wani abu da yake nuna hakan a zahiri.

Ko a lokutan baya ministan watsa labarai na Najeriya Lai Muhammad ya bayyana cewa, manyan kasashen turai ne basu son a kawo karshen boko haram, domin kuwa sun ki sayarwa Najeriya makaman da take bukata, duk kuwa da cewa ta karbi kudaden makaman.

Wadannan dukkaninsu abubuwa da suke saka alamar tambaya kan yadda wadannan manyan kasashen turai suke nuna halin ko in kula da wannan batu, wanda hakan zai zama dalilin da wasu ke ishara da shi na cewa wadannan kasashen suna amfana da abin da yake faruwa ta wasu hanyoyi da mutanen Najeriya ba su sani ba, domin kuwa ba tsron Najeriya ko zaman lafiyar al’ummarta ko ci gaban kasa ko habbakar tattalin arzikinta ne ya dami manyan kasashen turai ba, har kullum cimma manufarsu shi ne ke da muhimmanci fiye da komai, ko da kuwa za su saka rayuwar miliyoyin mutane cikin hadari.


015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!