​MDD: Ya Kamata A Kawo Karshen Yakin Kasar Yemen A Shekara Mai Kamawa

2020-12-28 18:58:30
​MDD: Ya Kamata A Kawo Karshen Yakin Kasar Yemen A Shekara Mai Kamawa

Babban manzon majalisar dinkin duniya a kasar Yemen Martin Griffiths ya bayyana cewa, lokaci da ya kamata a kawo karshen yakin kasar Yemen, ta hanyar samun fahimtar juna tsakanin dukkanin bangarorin siyasar kasar.

Ya ce yana da kyau bangarorin siyasar da suka hada da gwamnatin Hadi Mansur da kuma gwamnatin San’a karkashin jagorancin Ansarullah, su koma kan teburin tattaunawa, su samar da hanya guda ta sulhu da warware matsalolinsu.

Manzon majlaisar dinkin duniya ya kara da cewa, al’ummar Yemen ne kawai a tsakaninsu za su iya warware matsalolinsu na siyasa, ba tare da shigar shugula ta kasashen ketare ba.

Haka nan kuma ya kara da cewa, a shirye yake domin ya ci gaba da aikin sasanta bangarorin na kasar Yemen, domin samun zaman lafiya mai dorewa a kasar daga shekara mai kamawa, domin kuwa a shekara mai karewa babu abin da aka gani kasar sai kisa da yunwa da corona da kuma gudun hijira.

Ofishin majalisar dinkin duniya kan harkokin agaji ya bayar da rahoton cewa, daga lokacin da Saudiyya ta fara kaddamar da hare-hare a kan kasar Yemen a 2014, ya zuwa mutane dubu 233 ne suka rasa rayukansu a kasar.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!