An Zabi Cristiano Ronaldo A Matsayin Dan Wasan Kwallon Kafa Na Karni

2020-12-28 08:51:25
  An Zabi  Cristiano Ronaldo A Matsayin Dan Wasan Kwallon Kafa Na Karni

Dan wasan kwallon kafar dan asalin kasar Portugal ya sami kyautar zama mafi shaharar dan wasan kwallon kafa na karni, duk da cewa shekaru 20 ne kadai su ka shude a cikin wannan karni.

Gabanin zaben nashi, Cristiano Ronaldo ya lashe wasu kyautuka daban-daban da su ka hada da takalmin zinariya na hukumar kwallon kafa ta tarayyar turai da kuma wasu na kasarsa ta Portugal da Manchester United.

A yayin bikin mika masa kofi da aka yi a birnin Dubai, Cristiano Ronaldo ya yi godiya ga dukkanin wadanda su ka zabe shi domin girmama shi da wannan kyautar wacce ya ce za ta kara masa karfin gwiwa domin ci gaba.

013

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!