Ministan Tsaron Kasar Turkiya Ya Ja Kunnen Janar Halifa Haftar Na Kasar Libya Akan Gigin Kai Wa Sojojin Kasar Hari

2020-12-28 08:47:48
  Ministan Tsaron Kasar Turkiya Ya Ja Kunnen Janar Halifa Haftar Na Kasar Libya Akan Gigin Kai Wa Sojojin Kasar Hari

Ministan tsaron kasar Turkiya Hulusi Akar wanda ya kai ziyara kasar Libya a jiya Lahadi, ya bayyana cewa; matukar aka kai wa sojojin kasarsa hari to dukkanin cibiyoyin soja da ke gabashin kasar za su zama halartattun wuraren kai wa hari.

Akar wanda ya gabatar da taron manema labaru a birnin Tripoli a jiya Lahadi ya kara da cewa; Babbar matsalar da kasar Libya take fuskanta ita ce ta Halifa Haftar da mutanensa da su ka yi imani da cewa; Dole ne a sauya gwamnati ta hanyar amfani da karfi.

Ziyarar Akar zuwa Libya ta zo ne bayan da majalisar dokokin kasar Turkiya ta tsawaita wa’adin sake tura sojojin kasar zuwa Libya na wasu watanni 18 a nan gaba.

Libya ta fada cikin matsalar tsaro tun bayan da kungiyar yarjejeniyar tsaro ta “NATO” ta jagoranci kifar da gwamnatin Muammar Gaddafi a 2011.

Kasar mai arzikin man fetur ta rabe gida biyu a siyasance tsakanin gabashinta da yamma da ake da gwamnatoci daban-daban da kowane bangare yake samun goyon baya daga waje.

013

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!