An Yi Harbe-harbe Da Kai Hare-hare A Lokacin Zaben Kasar “Afirka Ta Tsakiya”

2020-12-28 08:44:24
An Yi Harbe-harbe Da Kai Hare-hare A Lokacin Zaben Kasar “Afirka Ta Tsakiya”

A jiya Lahadi ne aka gabatar da zaben shugaban kasar “Afirka Ta Tsakiya” da kuma na ‘yan majalisar dokoki a cikin tashe-tashen hankula da suka mamaye shi. Shugaban kasar Faustin Archange Touadera ya kada kuri’arsa a karkashin tsaro sojojin Rwanda da kuma dakarun MDD.

Dakarun MDD sun sanar da cewa sun dakile wani hari da masu dauke da makamai su ka kai a unguwannin Bria da Paoua da ke cikin babban birnin kasar a yayin da ake gudanar da zabe.

Kwanakin kadan da su ka gabata, kasashen Rwanda da Rasha sun aike da daruruwan sojojinta zuwa kasar ta “Afrika Ta Tsakiya’ domin dakile wani yunkuri na juyin mulki a yankin Bangui.

013

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!