Iran Ta Gano Amurkawa 48 Dake Da Hannu A Kisan Shahid Soleimani

2020-12-27 22:29:14
Iran Ta Gano Amurkawa 48 Dake Da Hannu A Kisan Shahid Soleimani

Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta ce yanzu haka ta gano AMurkawa 48 da suke da hannun a kisna da akayi wa Shahid Ghassem Soleimani yau kusan shekara guda data gabata.

Kwamitin dake shirya taron zagayowar ranar shahadar ta Janar din da Abu Mahdi al-Mohandes da wasu dake tare dasu, ya ce yana jiran matakin shari’a mai tsauri kan wadanda ke da hannu a kisan.

Iran dai ta ce har yanzu tana kan bakarta na cewa zata dauki fansa akan kisan da akayi wa Janar din nata shahid Ghassem Soleimani.

A ranar 3 ga watan Janairu na shekara 2020 din nan ne Janar Ghassem Soleimani ya yi shahada a wani hari da Amurka ta kaiwa tawagar motocinsa a kusa da filin jirgin saman Bagadaza na kasar Iraki, bisa umarnin shugaba Trump.

Tags:
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!