Nijar Na Kan Kafa Tarihi A Tsarin Demokuradiyya

2020-12-27 22:18:35
Nijar Na Kan Kafa Tarihi A Tsarin Demokuradiyya

Rahotanni daga jamhuriyar Nijar, na cewa an kai ga rufe runfunan zabe a wasu sassan kasar.

Bayanai sun kuma ce an samu fitowar jama’a sosai a zabubukan na yau duk da matsalolin tsaro a wasu sassan kasar da kuma annobar korona.

Bayan kada kuri’arsa, shugaban kasar mai barin gado Alhaji Isufu Mahamadu, ya bayyana ranar da mai cike da tarihi, kamar yadda a cewarsa ya yi alkawari na mika mulki ga wanda ‘yan kasar suka zaba, wanda shi ne karon a tarihin kasar cikin shekaru sintin data samu ‘yancin kai.

Shugaba Isufu, dan shekaru 68, ba ya takara a zaben kasancewar kundin tsarin mulkin kasar ya haramta masa hakan, bayan kammala wa’adinsa na biyu, sabanin wasu shuagabannin Afrika dake kwaskware kundin tsarin mulki domin ci gaba da mulki.

Kimanin ‘yan Nijar miliyan 7 da rabi ne ake kyautaton zaton zasu kada kuri’a a zaben shugaban kasa gami dana ‘yan majalisar dokoki a wannan kasa mai mutane kimanin miliyan 23 dake yankin sahel dake fama da matsalolin tsaro masu nasaba da mayakan dake ikirari da sunan jihadi.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!