CRA : MDD Ta Yi Tir Da Kisan Ma’aikatan Wanzar Da Zaman Lafiya

2020-12-27 22:11:16
CRA : MDD Ta Yi Tir Da Kisan Ma’aikatan Wanzar Da Zaman Lafiya

Babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya yi Allah wadai da babbar murya, kan hare-haren da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba, suka kaddamar kan ma’aikatan wanzar da lafiya na MDD a Jamhuriyar Afirka ta tsakiya (CRA).

Wata sanarwa da kakakinsa Stephane Dujarric ya fitar ta bayyana cewa, hare-haren na ranar Jumma’a kan dakarun tsaron kasar CAR da ma dakarun MDD dake aikin wanzar da zaman lafiya a kasar, sun kai ga halaka masu aikin wanzar da zaman lafiya uku ‘yan kasar Burundi tare da jikkata wasu guda biyu.

Dujarric ya ce, babban sakataren ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan ma’aikatan wanzar da zaman lafiyar da suka halaka, gami da gwamnati da al’ummar Burundi, tare da fatan samun sauki cikin hanzari ga wadanda suka jikkata.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!