Iran Ta Yi Tir Da Takunkumin Amurka Kan Jami’ar al-Mustapha

2020-12-27 14:45:46
Iran Ta Yi Tir Da Takunkumin Amurka Kan Jami’ar al-Mustapha

A wani bayani da dan majalisa Ruhullah Mutafakkir Azad ya karanta ya bayyana cewa; makiyan ci gaban ilimi sun sake nuna kansu a wannan lokaci, ta hanyar kai farmaki akan cibiya mai girma irin jami’ar Mustafah, wacce tana daya daga cikin muhimman cibiyoyin ilimi na duniya.

Bayanin ya ci gaba da cewa; Wannan irin matakin yana nuni ne da gajiyawar Amurka da yanke kaunarta akan ci gaban ilimi da al’ummar Iran take yi.

A makon da shude ne dai Baitul-malin Amurka ya sanar da kakaba takunkumi akan jami’ar Mustafa.

013

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!