Ana Zaben Shugaban Kasa A Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya

2020-12-27 14:42:45
Ana Zaben Shugaban Kasa A Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya

Muhimmin dan takarar shugabancin kasar shi ne Faustin Archange Touadera wanda aka zaba a 2016.

Kasar Afirka Ta Tsakiya, tana cikin daya daga kasashen nahiyar Afirka da suka dade suna fama a rikice-rikce siyasa.

Ayayin yakin neman zabe kasar ta tsunduma cikin rikici, inda aka yi zargin kokarin juyin mulki, bayan da wasu fandararrun sojoji su ka kwace iko da gari na hudu a wajen girka a kasar.

Sai dai kasashen Rasha da Rwanda sun aike da sojojinsu zuwa grin domin daikile yunkurin juyin mulkin da sake mayar da zaman lafiya mai dorewa.

Bayan barkewar yakin basasar kasar a 2013 dubban mutane ne suka rasa rayukansu, yayin da fiye da kaso ¼ na al’ummar kasar su ka gudu domin samun mafaka.

013


Comments(0)
Success!
Error! Error occured!