Wata Tawagar Moroko Za Ta Ziyarci H.K Isra'ila

2020-12-27 14:40:04
Wata Tawagar Moroko Za Ta Ziyarci H.K Isra'ila

A Jiya Asabar ne Pira Ministan HKI, Benamine Netenyahu ya sanar da cewa; Wata tawaga ta kasar Moroko za ta ziyarci Tel Avi domin bunkasa alaka da ‘yan sahayoniya.

Kamfanin dillancin labarun “Mehr” ya dauki labarin da cewa; Netenyahu ya wallafa a shafinsa na “Twitter” cewa; A ranar juma’ar da ta gabata ya yi Magana ta wayar tarho da sarkin Moroko Muhammad Sadisu, inda su ka cimma matsaya akan cewa Morokon za ta aike da tawaga zuwa Tel Aviv.

Munafar ziyarar tawagar dai kamar yadda Netenyahu ya bayyana shi ne bunkasa alaka a tsakaninsu.

A ranar Talatar makon da ya gabata, wata tawagar ta yahudawan Sahayoniya ta kai ziyarar kasar Moroko.

A cikin watannin bayan nan dai kasashen larabawa da dama su ka sanar da kulla alaka da HKI.

013

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!