Kungiyar Hamas Ta Dora Alhakin Duk Abin Da Ya Biyo Baya Kan Isra’ila Saboda Harin Da Take Kai A Yankin Gaza

2020-12-27 11:51:32
Kungiyar Hamas Ta Dora Alhakin Duk Abin Da Ya Biyo Baya Kan Isra’ila Saboda Harin Da Take Kai A Yankin Gaza

Rahotanni daga Gaza sun bayyana cewa Kungiyar gwagwarmar ta Hamas mai fafutukar yanto palasdinu ta dora alhakin dukkan abin da ya biyo baya kan Isra’ila sakamakon hare-haren da ta kai a daren jiya a yankin gaza. Inda da gangan ta harba makamai kan gidajen fararen hula.

A daren jiya ne sojojin HKI suka yi amfani da jiragen yaki wajen kai hare-hare a yankin gaza, musamman a muhimman wurare 3 na kungiyar Hamas, inda ta yi zargin cewa ta kai hari a wuraren ne saboda akwai kamfanonin kera makamai kuma tana ajiye kayayyakin soji a cewar ta.

Kakakin kungiyar ta Hamas Fawzi Barhum ya yi tir da mummunan harin rashin tausayi da HKI ta kai a yankin na Gaza, domin ta kai harin ne kan gidajen fararen hula da suka hada da Asibitoci da Makarantu, kana ya nuna cewa kulla dangantaka da Israila da wasu kasashen larabawa suka yi irin su Hdaddiyar daular larabawa ds, ya kara bawa Isra’ila lasisin ci gaba da zaluntar Alummar palasdinu.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!