Kungiyar Kwallon Kafa Ta Manchester City Ta Koma Ta 2 A Teburi Da Maki 26 A Gasar Premier

2020-12-27 11:43:07
Kungiyar Kwallon Kafa Ta Manchester City Ta Koma Ta 2 A Teburi Da Maki 26 A Gasar Premier

A ci gaba da wasannin da ake bugawa na gasar Premier a kasar Ingila,kungiyar kwallon kafa ta man city ta nuna wa Newcastlae cewa ruwa ba tsaran Kwando ba ne inda ta doke ta da ci 2-0 a wasan da sauka buga a jiya da dare. Wannan ya sa man city din ta koma ta 2 a teburi da maki 26.

Har yanzu dai kungiyar kwallon kafa ta Manchester united ita ce ke kan gaba a saman tebur da maki 27. sai kuma Aston villa a matsayin ta 3.

Haka zalika ita ma kungiyar kwallon kafa ta Chealse ta kwashi kashinta a hannun Arsenal da ci 3-1 a wasan da suka buga a jiya.

Brono Fenanders dan wasan kwallon kafa na farko dan kasar Fortigal da ya ci kwalliaye 10 a gasar Premiar tun bayan Cristiana Ronaldo.

Manajan Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jorgen Kloop ya bayyana cewa kungiyar ba za ta tilasta wa dan wasan gaban ta din nan Mohammad Sala ya ci gaba da buga mata wasa ba, don bai ga dalilan da za su sa ya bar kungiyar ba , shi dai salah a hira ra yayi da wata jaridar kasar Spain ya fadi cewa yana sha’awar kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid da Barcelona, wannan ya sa ake ganin wannan maganarce ta kara ruruta batun cewa zai bar kungiyar ta liver pool.


Comments(0)
Success!
Error! Error occured!