Taron Cikar Shekara 1 Na Shahadar Qassem Sulaimani Da Abu Mahdi Almuhandis

Za a gudanar da zaman taro dangane
da zagayowar lokacin cikar shekara guda da shahadar Janar Qasem Sulaimani da
kuma Abu mahdi Almuhandis.
Ma’ikatar raya al’adu ta kasar Iran
ta sanar da cewa, ofishinta da ke birnin Beirut na kasar Lebanon zai jagoranci
gudanar da zaman taro, wanda zai yi dubi kan cikar shekara guda shahadar manyan
kwamandoji biyu, Qassem Sulamani da kuma Abu Mahdi Almuhandis.
Wannan taro dai zai kunshi manyan
malamai da kuma masana gami da wakilan kungyoyi daban-daban a kasar Lebanon,
daga ciki har da wakilan kungiyoyin gwagwarmayar Falastinawa.
Babbar manufar wannan taro dai ita
ce ci gaba da raya tafarkin wadannan manyan kwamandoji biyu da suka yi shahada
wajen kare martabar addini, daga yunkurin makiya na bata sunan addinin muslucni
ta hanyar kirkiro ‘yan ta’adda masu kisan bil adama da sunan addini ko jihadi.
A shekarar da ta gabata ce Amurka
bisa umarnin shugaban kasar ta kai hari da jirgi maras matuki a kusa da filin
sauka da tashin jiragen sama na birnin Bagadaza, inda ta kashe Qassem Sulaimani
babban kwamandan dakarun Quds a Iran, da kuma Abu Mahdi Almuhandis mataimakin
babban kwamandan dakarun Hash Al-shaabi na Iraki.
015