Iran: Rauhani Ya Aike Da Sakon Taya Murnar Kirsimati Ga Shugabannin Kasashe

Shugaban kasar Iran Dr. Hassan
Rauhani ya aike da sakon taya murna ga shugabannin kasashe daban-daban kan
zagayowar lokain haihuwar annabi Isa (AS).
A cikin sakon nasa, shugaban kasar
Iran Dr. Hassan Rauhani ya bayyana cewa, duniya a halin yanzu tana bukatar yin
aiki na hadin gwiwa tsakanin dukkanin al’ummomi na duniya, domin tunkarar
abubuwan da suke a matsayin kalubale ga ‘yan adam baki daya, inda a halin yanzu
daya daga cikin misalign hakan shi ne yaki da cutar corona.
Haka nan kuma shugaba Rauhani ya yi
ishara da cewa, annabi Isa (AS) manzo ne daga cikin manzannin Allah, wanda ya
yada sulhu da da kaunar juna a tsakanin bil adama, wanda kuma wannan shi ne
tafarki na dukkanin annabawan Allah amincin Allah ya tabbata gare su, wato kira
zuwa ga tsira wanda hakan yana kunshe a cikin bin tafarkin ubangiji da kiyaye
dokokinsa.
Ya yi fatan alhairi ga takwarorinsa
na duniya, tare da yin fatan wannan shekara ta miladiyya mai kamawa ta zo ma
al’ummomin duniya da alhairi da albarka da yalwatar arziki da zaman lafiya.