Jibouti: Shugaba Guella Ya Ce Kasarsa Ba Za Kulla Alaka Da Isra’ila Ba

Shugaban kasar Jibouti ya bayyana
rashin amincewarsa da matakin da wasu kasashen larabawa suka dauka na kulla
alaka da Isra’ila.
Tashar Aljazeera ta bayar da rahoton
cewa, a zantawar da ta yi da shugaban kasar Jibouti Isma’il Umar Guella ya
bayyana cewa, wasu daga cikin kasashen larabawa sun kulla alaka da Isra’ila
bisa hujjar yarjejeniyar da kasashen larabawa suka cimmawa kan hakan.
Ya ce wadannan kasashe sun sabawa
wannan yarjejeniya, wadda tsohohon sarkin Saudiyya marigayi sarki Abdallah ya
gabatar da ita, wadda ta kunshi cewa, idan aka kafa kasashe biyu wato Falastinu
da Isra’ila, kowace mai cin gishin kanta, to a lokacin Larabawa za su iya
amincewa da Isra’ila a matsayin kasa.
Shugaban na Jibouti ya ce babu ko
daya daga cikin wadannan sharudda da suka tabbata, a kan haka babu dalilin
fakewa da sunan yarjejeiyar larabawa wajen kulla hulda da gwamnatin yahudawan
Isra’ila,a lokacin da take mamaye da Falastinu.
Haka nan kuma ya bayyana rashin
amincewarsa da hankoron wasu na mayar da tashoshin jiragen ruwa na yankin a
mjatsayin warare na aiwatar da siyasa, maimakon harkoki na kasuwanci da
tattalin arziki.
015