Jagoran Juyin Musulunci Na Iran Ya Taya Kiristoci Da Musulmi Murnar Zagoyowar Ranar Haihuwar Annabi Isa ( A.S)

2020-12-26 09:05:10
Jagoran Juyin Musulunci Na Iran Ya Taya Kiristoci Da Musulmi Murnar Zagoyowar Ranar Haihuwar Annabi Isa ( A.S)

Cikakken sakon Jagora Na Kirsimeti shi ne kamar haka:

Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Ina yi wa dukkanin mabiya addinin kirista da musulmi murnar zagoyowar wannan lokacin na haihuwar annabi Isa ( A.S), musamman kiristoci ‘yan kasa.

Annabin Allah ne zababbe wanda ya rika kiran mutane zuwa ga hanyar samun sa’ada, wacce ita ce hanyar Allah, da kuma gargadinsu akan biyewa son zuciya da nesantar aikata munanan ayyuka da zalunci da za gurbata tsarkin ruhinsu. Dawagitai masu mulki da kuma masu bautar abin duniya sun cutar da wannan annabin na Allah da kokarin kashe shi, sai dai Allah ya kiyaye shi da kare shi, sai su ka azabtar da mabiyansa ta hanya mafi muni, na shekaru masu tsawo domin su kawar da koyarwarsa wacce take fada da barna da zalunci da shirka da biyewa son zuciya da shelanta yake-yake. Mabarnata da azzalumai ba za su iya daurewa bin adinin Allah da annabinsa da hanyar Allah ba.

A wannan lokacin ma da masu takama da karfi wadanda ba a shirye su ke ba su jure ganin masu bautawa Allah, da biyayya ga addinin Alalh da neman gaskiya. Yin biyayya ga annabi Isa ( A.S) yana nufin taimakon gaskiya da barranta daga masu takama da karfi da kiyayya da gaskiya.

Ina fatan kiristoci da msulmi a ko’ina a duniya da su raya darussan raywuar annabi Isa (A.S) ma’abocin girma, a cikin raywarsu.

Ina rokon Allah ya sa sabuwar shekarar da za a shiga ta zama mafificiya ga dukkanin al’ummun duniya.

Sayyid Ali Khamnei

013

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!