Amurka: An Ga Sassan Jikin Mutum A Wurin Da Aka Kai Hari A Garin Nashville Na Kasar Amurka A Jiya Juma’a

2020-12-26 08:46:12
Amurka:  An Ga Sassan Jikin Mutum A Wurin Da Aka Kai Hari A Garin Nashville Na Kasar Amurka A Jiya Juma’a

Kafafen watsa labarun Amurka sun ambato majiyar tsaron kasar tana cewa an sami wasu sassan jikin mutum a wurin da aka kai hari da safiyar jiya Juma’a a tsakiyar garin Nashville da ke jihar Tennessee.

Ya zuwa yanzu dai jami’an tsaron ba su tantance ko sassan jikin na mutumin da ya kai harin ne ba, ko kuma na wanda aka kashe ne.

Da safiyar jiya Juma’a ta Kirsimeti ne dai wata mota mai makare da abubuwa masu fashewa ta tarwatse a garin na Nashville da ke jihar Tennessee, tare da jikkata mutane 3 da kuma lalata gidaje 20. Tuni dai hukumar bincike ta ‘yansandan kasar ( FBI) ta fara gudanar da bincike domin gano hakikanin abinda ya faru.

Masu bincike sun bayyana cewa ba a taba ganin hari mai girman wanda aka kai jiyan ba, a cikin kasar ta Amurka.

Tuni dai hukumar sufurin sana a garin ta dakatar da Zirga-zirga na wani lokaci, saboda tsinkewar hanyoyin sadarwa a cikin garin.

013

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!