Babban Limamin Maja’mirar Roman Katolika Na Duniya Ya Yi Kira Da A Samar Da Allurar Riga-Kafin Corona Ga Dukkanin Mutanen Duniya

2020-12-26 08:40:05
Babban Limamin Maja’mirar Roman Katolika Na Duniya Ya Yi Kira Da A Samar Da Allurar Riga-Kafin Corona Ga Dukkanin Mutanen Duniya

A cikin sakonsa na Kirsimeti a daren jiya Juma’a, Paparoma Francis ya yi kira da a samar da allurar riga-kafin ga kowa da kowa,musamman mutane da su ka fi zama cikin hadarin kamuwa da cutar da ko’ina a duniya.

Har ila yau, limamin majami’ar ta Roman Katolika ya tabo batun kananan yara da suke cikin halin kaka ni kayi, saboda yake-yake a kasashen Yemen, Syria da Iraki. Bugu da kari ya kira yi dukkanin mutane masu lamiri a duniya da su yi aiki tukuru domin kawo karshen yakin da ya cutar da wadannan yaran maza da mata.

Paparoma ya kuma kira yi shugabannin kasashe,‘yan kasuwa da kungiyoyi da su yi aiki cikin hadin kai, ba gasa ba, domin samo da mafita ga matsalolin da ake fuskanta a duniya.

013

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!