Fifa: An Soke Wasannin “Yan Kasa Da Shekaru 17 Na 2021

2020-12-26 08:36:32
Fifa:  An Soke Wasannin “Yan Kasa Da Shekaru 17 Na 2021

Hukumar Kwallon Kafa Ta Duniya ( FIFA) Ta Soke Wasannin Cin Kofin Duniya Na Matasa ‘Yan Kasa Da Shekaru 17 Saboda Cutar Corona

A wata sanarwa da ta fitar a shafinta na internet, hukumar wasannin kwallon kafar ta duniya ta ce; An soke dukkanin wasannin kwallon kafa na samari masu shekaru kasa da 17 maza da mata na shekarar ta 2021, maimakon haka za a yi shi ne a 2023.

Matakin na hukumar wasannin kwallon kafa ta duniya dai ya biyo bayan soke wasanni daban-daban da aka yi a duniya tun bullar cutar covid-19 a shekarar da ta gabata.Daga cikin wasannin da aka soke da akwai wasannin Olympic wanda aka shirya yi a kasar Japan.

Bullar cutar ta Covid-19 ta zama wani babban kalubale ga harkokin wasannin kasa da kasa.

013

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!