Iran Ta Bayyana Cewa; Palasdinu Ce Kadai Ta Sani A Matsayin Kasa Mai Babban Birni A Kudus
2020-12-25 20:14:57

Mai bai wa shugaban majalisar shawarar musulunci ta Iran shawara akan harkokin kasa da kasa, Husain Amir Abdullahiyan ne ya bayyana haka yana mai kara da cewa; Pira Ministan ‘yan sahayoniya Benjamine Natenyaho ya zo karshe a siyasance, kuma ‘yan sahayoniya ba su da wata rayuwa mai dorewa a cikin wannan yankin.
Abdullahiyan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da jakadan kungiyar Hamas anan Iran Khalid al-judumy, da kuma Nasir Abu Sharif wanda shi ne jakadan kungiyar Jihadul-Islami a Iran,yana mai kara da cewa; HKI wani tsari ne na bogi.
Har ila
yau, Abdullahiyan, ya mika gaisuwar shugaban majalisar shawarar musulunci ta Iran
Muhammad Baqir Qalibaf zuwa ga jagororin gwgwarmaya da al’ummar
Palasdinu.
Bugu da
kari,bangarorin biyu sun tattauna hanyoyin bunkasa alaka a tsakaninsu da kuma
halin da ake ciki a Palasdinu.
A wani
sashe na tattaunawar Abdullahiyan ya bayyana cewa; Iran ba ta yin furuci da
wata kasa ba a Palasdinu sai ta Palasdinawa,wacce kuma Kudus ne babban
birninta.
An nasu
bangarorin, jakadun kungiyoyin na Palasdinawa sun jaddawa ci gaba da
gwagwarmaya har zuwa ‘yanto da dukkanin palasdinu.
.013
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!