Cutar Corona Ta Kashe Jagoran “Yan Hamayyar Kasar Mai Sama’ila Cisse

2020-12-25 20:11:01
 Cutar Corona Ta Kashe Jagoran “Yan Hamayyar Kasar Mai Sama’ila Cisse

A yau Juma’a ne aka sanar da mutuwar Sama’ila Cisse a wani asibiti a kasar Faransa bayan da cutar crona ta kamashi.

Iyalan mamacin ne dai su ka fadawa kamfanin dillancin labarun kasar Farana na AFP cewa, jagoran ‘yan hamayyar ya rasu yana dan shekaru 71.

Shi dai Sama’ila ya kasance jagoran jam’iyyar hamayya wanda masu dauke da makamai su ka yi garkuwa da shi na tsawon watanni shida, bayan kama shi da suka yi a lokacin da yake yakin neman zabe a ranar 25 ga watan Maris a kusa da birnin Timbuktu dake Arewa maso yammacin kasar.

An sake shi ne a cikin watan Oktoba,tare da wasu ‘yan kasashen Faransa da Italiya da masu ikirarin jihadi su ka yi garkuwa da su, ta hanyar yin musayarsu da ‘yan ta’adda 200.

013

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!