An Kai Wa Ayarin Motocin Sojan Amurka A Iraki Hari

2020-12-25 19:48:29
An Kai Wa Ayarin Motocin Sojan Amurka A Iraki Hari

Tashar talabijin din al-mayadeen’ ta bayar da labarin cewa; an kai wa ayarin motocin sojan na Amurka farmaki ne a yankin Samawah dake gundumar Muthannah a kudancin Iraqi.

Majiyar tsaron Iraki ta tabbatar da cewa harin da aka kai wa ayarin sojojin na Amurka ya yi sanadin lalata daya daga cikinsu.

A wani labarin daga Iraqi, wani bom da aka dasa a gefen hanya ya lalata motar wani kamfani wanda ya kulla kwantiragi da sojojin Amurka.

Wani labarin daga Iraqi ya ambato majiyar tsaron kasar tana cewa; Sojoji sun kai farmaki akan daya daga cikin maboyar ‘yan ta’adda na Da’esh, tare da kame uku daga cikinsu da safiyar yau Juma’a. Majiyar ta kara da cewa kai harin da kuma kame ‘yan ta’addar ya biyo bayan wani cikakken bayanin sirri ne da ka samu akansu.

013

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!