Makaman Tsaron Sama Na Kasar Syria Sun Kakkabo Makamai Masu Linzami Da HKI Ta Harba A Yankin Humah

2020-12-25 19:44:36
Makaman  Tsaron Sama Na Kasar Syria Sun Kakkabo Makamai Masu Linzami Da HKI Ta Harba A Yankin Humah

Majiyar tsaron kasar Syria ta shaida wa kamfanin dillancin labarun kasar “ SANA” cewa; Da asubahin yau Juma’a ne HKI ta kai hare-hare akan yankin Misyaf da ke gundumar Humah, sai dai makaman tsaron samaniyar kasar ta Syri, sun kakkabo mafi yawancinsu.

Majiyar ta ci gaba da cewa; illar da hare-haren su ka yi wa yankin ba su da yawa, kuma na ci gaba da tantance su.

Tun da fari wata majiyar tsaro ta ambaci cewa an ga jiragen yakin HKI suna shawagi a kasa-kasa a saman birnin Beirut na kasar Lebanon da Jabalu-Lubnan da kuma yankin Matan.

Tun bayan da kasar Syria ta fada cikin yaki daga 2011, HKI take amfani da halin da kasar take ciki tana kai hare-hare daga lokaci zuwa lokaci.

A wasu lokuta hare-haren kan haddasa asara ta rayuka da kuma dukiya.

013

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!