Iran Ta yi Watsi Da Zargin Amurka Na Hannu A Harin Da Aka Kai Ofishin Jakadancinta A Iraki

2020-12-24 22:20:44
Iran Ta yi Watsi Da Zargin Amurka Na Hannu A Harin Da Aka Kai Ofishin Jakadancinta A Iraki

Ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Javad Zarfi ya yi wasti da zargin da shugaban Amurka mai jiran gaado Donald Trumph yi wa Iran na hannu wajen a harin roka-roka da aka kai a baya bayan nan a ofishin jakadancinta dake birnin Bagadaza.

A ranar Lahadin da ta gabata ce wasu makaman roka guda 3 Samfarin Katusha suka fada da karfin gaske a wani wuri da aka killace kusa da ofishin jakadancin Amurka dake Iraki, duk da naurar kariya tunkude daya daga cikin makamin rokan domin kare ofishin jakadancin, inda a ranar Laraba kuma Trumph ya yi barazanar dora alhakin harin da aka kai kan kasar Iran

Har ila yau Zarif ya kara da cewa shugaban na Amurka ya bijori da wannan zargin ne domin kawar da hankalin duniya kan gazawarsa a tsawon lokacin shugabancin Amurka, domin sanya yan kasarsa cikin hatsari a waje, ba zai kawar da hankula game da gazawarka a fili a cikin gida ba.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!