Hukumar Jami’an Farin kaya SSS a Nigeria Ta Yi Gargadi Game Da Yiwuwar Kai Hare-haren Ta’addanci A Lokacin Kirsimeti

2020-12-24 22:18:08
Hukumar  Jami’an Farin kaya SSS a Nigeria Ta Yi Gargadi Game Da Yiwuwar Kai  Hare-haren Ta’addanci A Lokacin Kirsimeti

A cikin wata sanarwa da kakakin hukumar ta SSS Peter Afunaya ya fitar da gargadi mutane da su yi taka tsantsan saboda akwai yiwuwar kai hare-hare da tayar da bom a lokacin bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara a Najeriya.

Har ila yau ya ci gaba da cewa mutane su yi taka tsantsan da kuma sa ido musmaman idan za su shiga wajen da ke da cunkoson jama’a, domin masu dana bom sun fi shiga inda jama’a su ka fi taruwa.

Ya kara da cewa ana hasashen kai hare- hare da tada bama-bamai din ne a wuraren da babu wadatacccen tsaro domin yi wa gwamnatin tarayya kafar-ungulu kan namijin kokarin da take yi wajen tabbatar da tsaro a fadin kasar.

Daga karshe hukumar ta SSS ta fadi cewa suna aiki da sauran bangarorin tsaro na kasar wajen ganin sun dakile duk wani yunkurin kai harin ta’adanci da kuma tabbatar da tsaro da kare rayuka da dukiyoyin alumma.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!