Yan Majalisa 150 Na Demokrat A Amurka Sun Bukaci Biden Ya Koma cikin Yarjejniyar nukiliyar Iran

2020-12-24 22:11:44
Yan Majalisa 150 Na Demokrat A Amurka Sun Bukaci Biden Ya Koma cikin Yarjejniyar nukiliyar Iran

Rahotanni sun bayyana cewa kimanin yan majlisar wakilai na kasar Amurka guda 150 ne da suka fito daga Jam’iyar Demokrat suka yi Kira ga sabon shugaban kasar ta Amurka Joe Biden da ya koma cikin tatttaunawar nukiliyar kasar iran da aka cimma matsaya kai. A wani mataki na yin hannun riga da na shugaban Amurka Donald Trumph mai barin gado, in da a rana tsaka ya fice daga cikin yarjejniyar nukiliyar jim kadan bayan rattaba hannu akai.

A watan Yulin shekara ta 2015 ne kasar Iran da sauran kasashen masu karfi guda 6 wato Amurka, Fransa, Rasha, China da kasar Jamus suka rattaba hannun kan yarjejeniyar nukiliyar kasar Iran da suka cimma matsaya akai, bayan kwashen dogon lokaci ana tattaunawa akai, sai kwatsam Amurka ta fice daga kawancen kuma ta sake kakaba takunkumi kan kasar Iran da kuma dawo da wadan da aka dauke a baya.

Wannan mataki da kuma kasa tabuka komai daga bangaren kasahen turai suka yi na kulla huldar kasuwanci da Iran, ya sa ta fara rage aiki da yarjejeniyar da aka cimma.

Iran ta bukaci sabon shugaban Amurka da ya biya ta diyyar asarorin da Amurka ta jawo wa ma ta sakamakon ficewarta daga yarjejeniyar da aka kulla ta 2015.


Comments(0)
Success!
Error! Error occured!