Kungiyar Kwallon Kafa Ta Liverpool Ta ce Ba Ta Da Nufin Sayar Da Mohammad Salah

2020-12-24 22:08:42
Kungiyar Kwallon Kafa Ta Liverpool Ta ce Ba Ta Da Nufin Sayar Da Mohammad Salah

Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Jurgen Klopp, ya bayyana cewa kungiyar ba ta da wani shiri na cefanar da dan wasan gabanta Muhammad Salah, duk kuwa da jita-jitar da wasu ke yadawa ta yiyuwar yin hakan.

A karshen makon jiya ne dan wasan gaban na Liverpool, ya bayyana cewa akwai yiwuwar ya dena taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Liverpool a nan gaba kadan, a daidai lokacin da kungiyar ke komawa matsayin ja gaba na lashe gasar Firimiya ta kasar Ingila karo na biyu a jere.

A wata tattaunawa da wata jarida ta yi da abokin dan wasan mai suna Mohammad Abotrika ya fadi cewa Salah ya nuna bacin ransa sosai game da yadda kungiyar ta ki ba shi matsayin Kyaftin a wasan da suka buga na gasar cin kofin zakarun kasashen turai, sai kawai aka bawa abokin wasansa Trent Aledendra ya jagorancin wasan, wannan ya sa ya fara tunani canza sheka zuwa wani club din.


Comments(0)
Success!
Error! Error occured!