​Amurka: Musulmi Sun Bukaci Biden Da Ya Janye Dokar Leken Asiri A Kansu

2020-12-24 14:19:10
​Amurka: Musulmi Sun Bukaci Biden Da Ya Janye Dokar Leken Asiri A Kansu

Kwamitin musulmin kasar Amurka ya bukaci zababben shugaban kasar da ya janye dokar da Trump ya kafa ta yin leken asiri a kan musulmi.

A rahoton da kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga Tashar Fox News an bayyana cewa, a cikin bayanin da kwamitin musulmin kasar Amurka ya fitar, ya bukaci zababben shugaban kasar ta Amurka Joe Biden, da ya sanya batun janye dokar da Trump ya kafa ta yin leken asiri a kan musulmi a matsayin daya daga cikin abubuwan da zai fara yi a cikin kwanaki dari na farkon mulkinsa.

Bayanin ya ce bisa la’akari da yadda Trump ya kafa dokar takura musulmi da hana su sakat a cikin Amurka da sunan yaki da ta’addanci, ya kamata Biden ya janye wannan dokar domin dawo da martabar dimukradiyya a kasar Amurka.

An kafa dokar ne da ke yin leken asiri kan musulmi da kuma sanya idi a kansu da dukkanin harkokinsu, kamar yadda kuma jami’an liken asirin Amurka suke sanya ido a kan masallatai da cibiyoyi na addinin musulunci a fadin Amurka, domin ganin abin da musulmi suke yi a ciki.

Haka nan kuma kwamitin musulmin na Amurka ya bukaci Biden da ya yi wani abu domin kawo karshen takura wa musulmi a kasar China, da India da kuma Myanmar.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!