Iran Da Sweden Na Son A Kawo Karshen Zubar Da Jini A Yemen

2020-12-24 10:29:48
Iran Da Sweden Na Son A Kawo  Karshen Zubar Da Jini A Yemen

Kasashen Iran da kuma Sweden, sun jadadda wajabcin yin hadin guiwa domin kawo karshen rikici a kasar Yemen.

Bangarorin sun bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa ta kafar bidiyo, ta tsakanin babban mai taimakawa ministan harkokin wajen Iran kan harkokin siyasa na musamman, Ali-Asghar Khaji, da kuma wakili na musamman na kasar Sweden a yankin gabas ta tsakiya da kuma arewacin Afrika (MENA) Peter Semneby.

Kasashen biyu dai sun tattauna ne kan halin da ake ciki a kasar Yemen, ta fuskar siyasa da kuma jin kai.

A yayin tattaunawar ne jami’an kasashen biyu suka jadada wajabcin yin hadin guiwa domin magance rikicin kasar ta Yemen, da ya hada da isar da tallafin jin kai ga al’ummar Yemen musamman a wannan lokaci na fama da annobar cutar korona.

Iran dai na mai zargin kawancen da Saudiyya ke jagoranta da sabawa yarjejeniyar Stockholm, wanda ya kawo cikas wajen aiwatar da ita.

Kan hakan ne Iran din ta bukaci a farfado da yarjejeniyar tare da taimakon kasa da kasa ta yadda za’ayi aiki da ita.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!