AU Ta Tura Masu Sanya Ido A Zabukan CAR Da Nijar

2020-12-24 10:27:03
AU Ta Tura Masu Sanya Ido A Zabukan CAR Da Nijar

Kungiyar Tarayyar Afirka(AU) ta tura jami’an da za su sanya ido a manyan zabukan da aka shirya gudanarwa a kasashen Jamhuriyar Afirka ta tsakiya da kuma Nijar, a ranar 27 ga watan Disamban nan da muke ciki.

Tawagogin da kungiyar ta tura tun daga ranar 21 har zuwa 31 ga watan Disamba, sun kunshi masu sanya ido a harkokin zabe, da kwararru da kuma jami’an hukumar gudanarwar kungiyar.

Tsohon firaministan kasar Mali, Modibo Sidibe, shi ne zai jagoranci tawagar da aka tura Jamhuriyar Afirka ta tsakiya, yayin da tsohon firaministan Mauritaniya, Sghair Ould M’Bareck zai kasance jagoran tawagar da aka tura kasar Nijar.

Tura tawagogin zuwa kasashen biyu dai, yana kunshe ne cikin tanade-tanaden dokokin kungiyar game da manufofin tafiyar da zabe bisa tsarin demokiradiya a Afirka, da ka’idojin kungiyar AU game da sanya ido kan harkokin zabe, da tawagar sanya ido, gami da dokar tsarin demokuradiya a Afirka, zabuka da tafiyar da harkokin shugabanci.

Ayyukan tawagogin sun hada da, bayar da sahihan rahotanni game da manyan zabukan ba tare da nuna son kai ba, da martaba tsarin gudanar da zabukan demokuradiya daidai da mizani na kasa da shiyya, da nahiya da kasa da kasa.

Kafin hakan dama kungiyar ECOWAS, ita ma ta aike da tawagarta ta masu sanya ido a Jamhuriyar Nijar, data kunshi mambobi 90 karkashin jagorancin tsohon matakaimakin shugaban kasar Najeriya, Namadi Sambo.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!