MDD:Kayayyakin jin kai sun fara shiga yankin Tigray na Habasha

2020-12-24 10:24:09
MDD:Kayayyakin jin kai sun fara shiga yankin Tigray na Habasha

Majalisar Dinkin duniya ta sanar da cewa kayayakin jin kai sun fara isa a yankin Tigray na kasar Habasha dake fama da rikici.

Mai magana da yawun babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya bayyana a jiya Laraba cewa, sannu a hankali kayayyakin taimakon jin kai sun fara isa yankin Tigray na kasar Habasha, koda yake ba ko ina a wuraren da ake ci gaba da tashin hankali ake iya shiga ba.

Jami’in ya ce, hukumar lafiya ta duniya ta tura isassun kayayyakin lafiya da za a iya jinyar marasa lafiya sama da 10,000 har na tsawon watanni uku, baya ga karin kayayyakin lafiyan dake tafe.

A wannan mako ma shirin samar da abinci na duniya, ya samu damar kai kayan abinci ga ‘yan gudun hijira 35,000 dake sansanonin Adi Harush da Mai Ayni.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!