MDD Za Ta Janye Dakarunta A Yankin Darfur Na Sudan

2020-12-24 10:21:04
MDD Za Ta Janye Dakarunta A Yankin Darfur Na Sudan

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da kawo karshen aikin dakarun majalisar da na Tarayyar Afirka a lardin Darfur na Sudan daga ranar 31 ga watan Disamba, bayan karewar wa'adin da aka tsara na dakarun.

Da gagarumin rinjaye aka kada kuri'ar na rashin tsawaita lokacin dakarun na kiyaye zaman lafiya sakamakaon matsin lamba daga gwamnatin wucin gadin Sudan da Rasha gami da wasu kasashen Afirka.

Tun shekara ta 2007 dakarun kiyaye zaman na Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar Tarayyar Afirka suke aiki a lardin na Darfur da ke yamamcin Sudan. Akwai sojoji da 'yan sanda 6,000 gami da ma'aikata fararen huka fiye da 1,500.

Ita dai kasar ta Sudan tana kan hanyar komawa tafarkin dimukuradiyya tun bayan kawo karshen gwamnatin Shugaba Omar al-Bashir a watan Afrilun shekarar 2019.

Rikicin na Darfur ya kai ga mutuwar kimanin mutane 300,000 yayin wasu milyan biyu suke tsere daga gidajensu.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!