Wa’izy: Tehran A Shirye Take Ta Taka Rawa Wajen Warware Rikicin Baku Da Yerevan
2020-12-23 20:22:36

Shugaban ofishin shugaban kasar Iran, Mahmud Wa’izy ya bayyana farin cikinsa akan kawo karshen yaki a tsakanin kasashen Azerbaijan da Armenia, sannan ya kara da cewa; Iran din a shirye take ta taka rawa wajen kawo karshen sabanin da kasashen biyu suke da shi baki daya.
Wa’izy
wanda ya gana da mataimakin pira ministan kasar Azerbaijan ya ci gaba da cewa; Iran ta yi imani da cewa
wajibi ne a samo hanyar warware sabanin dake tsakanin kasashe, musamman masu
makwabtaka da juna ta hanyar diplomasiyya ba ta yaki ba.
Har ila yau, Mahmud Wa’izy ya ce; Yin taruka da za su kunshi Iran, Rasha, Azerbaijan, Turkiya da Armenia za su taimaka wajen kusantar juna da kuma ci gaban tattalin arziki.
A nashi gefen,
mataimakin Pira ministan kasar ta Azerbaijan, ya sanar da cewa; shugaban
kasarsu Ilham Alivey, ya yi imani da cewa ya kamata a ce iyakar kasashen biyu
ta zama ta zaman lafiya da kwanciyar hankali.”
Har ila yau
ya kara da cewa; Shugaban kasar ta Azerbaijan yana yin jinjina da godiya ga
jamhuriyar Musulunci ta Iran da jagororinta akan matsayar da suka dauka dangane
da sabani da kasar Armenia.
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!