A Karon Farko Kungiyoyin Gwagwarmanar Palasdianwa Sun Sanar Da Yin Atisaye Na Hadin Gwiwa

2020-12-23 20:20:39
A Karon Farko Kungiyoyin Gwagwarmanar Palasdianwa Sun Sanar Da Yin Atisaye Na Hadin Gwiwa

Kungiyoyin na gwagwarmayar Palasdinawa sun bayyana cewa; Atisayen na hadin gwiwa an y shi ne domin kara zaman cikin shirin ko-ta-kwana na yaki wanda shi ne irinsa na farko.

Sanarwar ta ci gaba da cewa anan gaba a lokacin da ya dace za a fitar da cikakken bayani akan yadda atisayen ya kasance.

A gefe daya, sojojin sahayoniyar da cewa sun yi kutse cikin gidajen Palasdinawa tare da kame wasu samarin a yankuna daban-daban na yammacin kogin Jordan.

Ita kuwa majiyar Palasdinawa ta ce ‘yan sahayoniyar sun yi kutse ne a cikin garin Qabadiyah dake kudancin Jenin, inda aka yi taho mu gama mai tsanani tsakanin sojojin HKI da matasan garin.

A garin Ramallah Yahudawa ‘yan share wuri zauna sun jikkata wani matashi mai suna Muhammad Subhi al-Unsawy, bayan da su ka taka shi da mota.

Kutsawa ckin birane da garuruwan Palasdinawa wani abu ne da ya zama ruwan dare, wanda ‘yan sahayoniya su ke yi daga lokaci zuwa lokaci.

013

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!