Shekarar Bana Ta 2020 Ta Zo Da Sauye-Sauye A Fagen Wasanni A Nahiyar Afirka

2020-12-23 20:12:11
Shekarar Bana Ta 2020 Ta Zo Da Sauye-Sauye A Fagen Wasanni A Nahiyar Afirka

Farkon wannan shekara ta 2000, ‘yan wasa daban-daban daga nahiyar Afirka sun yi taro a kasar Masar domin murnar shiga sabuwar shekara tare da shugaban kungiyar wasannin kwallon kafa ta nahiyar Ahmad Ahmad.

Sai dai duk da wancan kyakkyawan fatan na cewa za a gudanar da wasanni a cikin shekarar ta bana, ba a yi wasan cin kofin nahiyar Afirka a Kamaru ba, ko kuma wasannin Olympic a kasar Japan.

Bullar cutar Corona a kasar Sin da yaduwarta a duniya musamman daga watan Janairu, ya sauya harkokin wasanni a cikin nahiyar ta Afirka da ma duniya baki daya.

Shi kanshi shugaban hukumar kwallon kafa ta nahiyar Afirkan Ahmad Ahmad ya fuskanci dakatarwa a lokacin da yake son a sake zabarsa a wani zangon saboda samunsa da almubazzaranci da kudin hukumar. Don haka mutumin da ya gaji Isssa Hayatu, bai sami wani zabi ba da ya wuce yin murabus da barin shugabancin hukumar a hannun Constant Omari.

A fagen wasan kwallon Kwando kuwa dan kasar Nigeria a kasar Girka Giannis Antetokoumpo aui ya sake zama zakara shekaru biyu a jere,ya kuma rubuta kwantiragin shekaru biyar da da kudin da suka kai dalar Amurka 230.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!