Najeriya : Kungiyar ASUU Ta Janye Yajin Aiki

2020-12-23 15:05:01
Najeriya : Kungiyar ASUU Ta Janye Yajin Aiki

Kungiyar malaman jami'o'i ta Najeriya cewa da ASUU ta janye yajin aikin data kwashe kusan wata tara tana yi.

Rahotanni daga Najeriyar sun ce an cimma yarjejeniya tsakanin gwamnati da kungiyar bayan shafe sa'o’i takwas suna tattaunawar sirri a Abuja.

Yayin tattaunawar gwamnati ta amince biyan malaman jami’o’in naira biliyan arba’in na alawus da kuma wasu naira biliyan talatin na gyare-gyaren jami'o'i.

Yajin aikin da malaman jami’o’in na Najeriya suka kwashe wata tara sunayi ya dai jefa daliban jami’o’in kasar cikin halin ni ‘yasu.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!