Dan Bindiga Ya Kashe Jami’an Tsaro 3 A Faransa

2020-12-23 15:00:23
Dan Bindiga Ya Kashe Jami’an Tsaro 3 A Faransa

Wani dan bindiga ya kashe jami’an tsaro na Jandarma uku da kuma jikkata guda a wani kauye dake Lardin Puy-de Dôme dake tsakiyar Faransa.

Lamarin dai ya faru ne bayan an nemi agajin jami’an tsaron zuwa wani gida da aka samu rahoton cin zarafi.

Daga bisani dai an ce an samu gawar dan bindigan mai shekaru 48, da ya tsare bayan faruwar lamarin.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!