​Morocco: Sarki Muhammad Na 6 Ya Jinjina Wa Netanyahu Kan Karfafa Alaka A Tsakaninsu

2020-12-23 10:00:07
​Morocco: Sarki Muhammad Na 6 Ya Jinjina Wa Netanyahu Kan Karfafa Alaka A Tsakaninsu

Sarkin kasar Morocco Muhammad na 6, ya jinjina wa firayi ministan gwamnatin Isra’ila Benjamin Netanyahu, kan abin da ya kira ci gaban da suka samu wajen karfafa alaka a tsakaninsu.

Sarkin na Morocco ya bayyana hakan ne a daren jiya, a lokacin da yake ganawa da wata tawagar hadin gwiwa ta Amurka da Isra’ila da ta isa kasar Morocco a jiya, a karkashin jagorancin Jared Kushner babban mai bawa Trump shawara, da kuma shugaban majalisar tsaro ta Isra’ila Meir Ben Shabat.

A yayin ganawar, sarkin na Morocco ya bayyana cewa, karfafa alaka tsakanin gwamnatin Morocco da kuma Isra’ila yana da matukar muhimmanci, kuma yana jinjina wa firayi ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu kan hakan.

A nasa bangaren shugaban majalisar tsaro ta Isra’ila Meir Ben Shabat ya bayyana cewa, alakarsu da kasar Morocco tana gagarumin muhimamnci ga Isra’ila, ya kuma mika sakon gayyata zuwa Isra’ila, da Netanyahu ya aike wa sarkin an Morocco.

A yayin ziyarar an rattaba hanu kan yarjejeniyoyi daban-daban tsakanin gwamnatin Morocco da kuma gwamnatin yahudawan Isra’ila, da hakan ya hada da janye visa a tsakaninsu ga jami’an diflomasiyya, da ma’ikata da kuma masu saka hannayen jari, kamar yadda kuma suka sanya hannu kan fara zirga-zirgar jiragen sama na fasinja a tsakaninsu.


015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!