​Najeriya: Zulum Ya Nuna Rashin Gamsuwa Dangane Da Yanayin Tsaro

2020-12-23 09:37:58
​Najeriya: Zulum Ya Nuna Rashin Gamsuwa Dangane Da Yanayin Tsaro

Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum ya bayyana yawaitar garkuwa da jama’ar da ake samu a kan babbar hanyar Maiduguri zuwa Damaturu, da cewa gazawa ce ta sojojin Nijeriya wajen sauke nauyin da ya rataya a kansu na kare rayuka da dukiyar al’umma.

Zulum ya yi wannan furucin ne a lokacin da ya ziyarci inda wasu mahara suka yi awon gaba da matafiya 35 a kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu, hanya daya mai lafiya ta rage zuwa jihar Borno.

Da yake ganawa da manema labarai a wurin, Gwamna Zulum ya bayyana matukar bacin ransa dangane da faruwar al’amarin, duk da yadda aka jibge dimbin jami’an tsaro daban-daban a kan hanyar, amma a cewarsa hakan bai magance irin wadannan hare-hare a kan babbar hanyar ba.

“Gaskiya wannan babban abin bakinciki ne dangane da yadda ake ci gaba da awon gaba da matafiya tare da kashe su a wannan hanya ta Maiduguri har zuwa Kano, musamman tsakanin Maiduguri da Damaturu.

Bayan sace daliban sakandare ta Kankara a jihar katsina ne kuma aka sace wasu matafiya 35 a kan hanyar Damaturu Maidugiri, wanda ake sa ran ‘yan ta’adda na Boko Haram ne suke da hannu wajen sace mutanen, wadanda har yanzu ba a san makomarsu ba.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!