​An Dakatar Da Dukkanin Harkokin Shige Da Fice A Kasar Saudiyya

2020-12-23 09:30:09
​An Dakatar Da Dukkanin Harkokin Shige Da Fice A Kasar Saudiyya

Mahukuntan kasar Saudiyya sun sanar da dakatar da dukkanin harkokin shige da fice a kasar sakamakon bullar sabuwar cutar corona.

A cikin wani bayani da gwamnatin kasar ta Saudiyya ta sanar, ta bayyana cewa an dakatar da dukkanin harkokin shige da fice a kasar zai shafi dukkanin harkokin zirga-zirga na jiragen sama da suke shiga kasa daga kasashen ketare, kamar yadda jiragen kasar ma ba za su yi tafiya zuwa wata kasa ba.

Haka nan kuma mahukuntan na masarautar Saudiyya sun cewa, wannan doka za ta shafi bangaren harkoki na jiragen ruwa da kuma iyakoki na kasa, domin tabbatar da cewa babu shiga babu fita a kasar.

Sai dai dangane ad jirage na kasashen ketare da suke a cikin kasar a lokacin sanar da wannan doka za su iya ficewa zuwa kasashensu a duk lokacin da suke bukata.

Saudiyya ta dauki wannan matakin ne bayan da sabuwar cutar corona da ta bulla a kasar Burtaniya take kara tsanata, tare da fargabar cewa zata iya bazuwa zuwa sauran kasashen duniya.

Wannan lamari dai ya shafi harkokin ziyarar Umrah kai tsaye, da ma damar da aka samu a cikin ‘yan kwanakin baya bayan nan na yin ziyara a masallacin harami mai alfarma a birin Makka da kuma masallacin manzo (SAW).

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!