Zarif: Yin Amfani Da Siyasa Wajen Wareware Matsalar Afghanistan Ne Zai Samar Da Zaman Lafiya Mai Dorewa
2020-12-22 22:25:40

Ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Javad Zarfi ya fadi hakan ne a lokacin wata ganawa da ya yi da mai bawa shugaban kasar Afghanistan shawara kan tsaron kasa Hamdullah Muhib a ziyarar da ya kawo Iran yau, kuma ya kara da cewa nuna goyon bayanmu ga kasar Afghanistan dake makwabtaka da mu yana daga cikin tushen manufofin jamhuriyar musulunci a Iran.
Har ila
yau ya fadi cewa muna goyon bayan cimma matsaya ta hanyar siyasa da hadin
guiwar dukkan bangarorin da basa ga maciji da juna a kasar, wanda hakan zai bada
tabbatacen zaman lafiya mai dorewa a kasar. Kana ya bukaci ficewar dukkan dakarun Amurka daga kasar
da yaki ya yi wa yankan kauna.
Anasa
bangaren Hamdullah Muhib ya yi jinjina
game da irin goyon bayan da kasar Iran take ba wa gwamnatin kasar Afghanistan
da ma alummar kasar baki daya,kana ya yi kira da akara fadada danganatakar
siyasa, tattalin arzi, al’adu da tsaro
tsakanin kasahen biyu.
Da yake ishara game da layin dogo na Khaf –Herat da aka bude ya bayyana fatansa na ganin hakan ya karara dankon zumunci tsakanin kasashen biyu.
Tags:
ministan harkokin wajen kasar iran mohammad javad
mai bawa shugaban kasar afghanistan shawara kan ts
hamdullah muhib
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!