Pakistan: Ba Zamu Kulla Dangantaka Da HKI Ba Matukar Ba’a Warware Matsalar Palasdinawa ba

2020-12-22 22:21:07
 Pakistan: Ba Zamu Kulla Dangantaka Da HKI Ba Matukar Ba’a Warware Matsalar Palasdinawa ba

Ministan harkokin wajen kasar Pakistan Sha Mahmood Quraishi ya shaidawa Hadaddiyar Dalula Darabawa matsayin kasarsa game da batun kulla duk wata alaka da HKI , inda ya nuna cewa kasarsa ba za ta amince da duk wani batun kulla alaka da HKI ba matukar ba’a warware batun yankin palasdinu da ta mamaye ba.

Shi dai Quraishi ya kai ziyara ne a Hadaddiyar Daular Larabawa a ‘yan kwanakin nan, inda ake yada jita - jitar cewa kasar na shan matsin lamba daga Saudiya da Hadaddiyar Daular Larabawa na su dawo da alaka da HKI.Wannan ya sa ministan harkokin wajen ya fito fili ya bayyana matsayar kasar game da wannan batun.

Har ila yau ya kara da cewa matukar ba’a fitar da kwakkwaran mataki na kawo karshen mamayar da Isra’ila ta yi wa yankin palasdinu ba to ba za su taba kulla duk wata dangantaka tsakaninta da HKI ba.

Kasar Pakistan dai tana daga cikin kasahe 13 da musulmi suka fi rinjaye da hadaddiyar daular larabwa ta hana basu visar shiga kasarta.


Comments(0)
Success!
Error! Error occured!