Kasar Moroko Ta Sanar Da Kafa Dokar Hana Zirga-Zirga Na Tsawon Makwanni 3 A Fadin Kasar
2020-12-22 22:18:35

Ganin yadda cutar korona ke ci gaba da yaduwa a kasar ta Moroko, ya sa mahukumtan kasar fitar da sanarwa kafa dokar hana fita na tsawon Makwanni 3 da suka hada da rufe gidajen sayar da abinci da manyan kantunan sayar da kayan masarufi da kuma wuraren shan Gahawa, musamman a mayan biranen kasar kamar Casablanca da Marrakesh.Har ila yau an hana duk wani taron jama’a na gama gari ne ko kuma na daidaiku har ma da shirya bukukuwa.
Gwamnatin
kasar ta sanar da gano mutane 2000 da suka kamu da cutar ta korona a fadin
kasar. Ya zuwa yanzu mutane 400,000 ne aka tabbatar da sun kamu da cutar yayin
da 7000 kuma suka rasa rayukansu.
Wannan
yana zuwa ne adaidai lokacin da kasar ta Moroko ta mayar da zirga -zirgar
jragen sama tsakanin ta da HKI , inda tuni jirgin farko ya ta shi dauke da wani babban jami’i a fadar white House da kuma jakadan HKI a Moroko David Friednman.
Kasar
Moroko dai ita ce kasar larabawa ta 4 da ta mayar da alaka tsakaninta da HKI
bayan hadaddiyar daular larabawa, Bahrain, sai kuma kasar Sudan.
Tags:
kasar moroko
ta sanar da kafa dokar hana zirga-zirga
cutar korona ke ci gaba da yaduwa a kasar
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!