Dan Wasan Kwallon Kafa Na Barcelona Messi Ya Lashe Kyautar Zaman Lafiya Ta 2020

2020-12-22 22:16:03
Dan Wasan Kwallon Kafa Na Barcelona Messi Ya Lashe Kyautar Zaman Lafiya Ta 2020

Lionel Messi dan wasan kwallon kafa na Kasar Argentina kuma mai buga wasa a Barcalona shi ne aka ba wa kyautar zaman lafiya ta wannan shekarar ta 2020 saboda yadda yake buga wasa mai tsafta, da kuma iya mua’mala. Cibiyar Monako ta kasa da kasa dake ba da kyautar ta ce gidauniyar Lionel Messi ta taka muhimmiyar rawa a kasar Argentina wajen habaka Ilimi da da kuma taimaka wa yara marasa galihu a kasashen duniya daban daban.

Har ila yau dai dan wasan ya sake lashe kyautar dan kwallon da ya fi zura kwallaye a kakar wasan bana, wannan dai shi ne karo na 7 da ya lashe wannan kyauta da ake ba wa dan wasan da ya fi zura kwallaye a wasan La –liga, ko a kakar da ta wuce ma ya zuwa kwallye 25.

Daga karshe kuma za ku ji cewa a yau za’a buga wasanni guda 4 na Laliga in da za’a kece raini tsakanin Elche da Osasuna, sai kuma Valancia da Sevilla, sai kuma Raal Sociedad da Atletico Madrid, da Huesca da Lavente.

A wasan Seri –A, kuma za’a yi wasannin biyu ne kawai wato tsakanin Crotine da Parm sai kuma Juventus da Fitorentina . A gasar EFL ta birtaniya kuma za’a buga wasan kusa da gab da na karshen a yau tsakanin Brentford da Newcastle sai kuma Arsenal da Man City.


Comments(0)
Success!
Error! Error occured!